Informações:
Sinopse
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episódios
-
Barista Abba Hikima kan tsarin kiranye ga ƴan majalisu a dokokin Najeriya
27/03/2025 Duração: 03minA farkon makon nan, Hukumar Zaɓen Najeriya INEC, ta ce ba a kammala cika ƙa'idojin da kundin tsarin mulki ya gindaya ba, a kan tsarin kiranyen da ake ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattijai. INEC ta bayyana haka ne, bayan da ta fara nazari akan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata na nemn yi wa Sanata Natasha yankan ƙauna, wadda a kwanakin baya ta zargi shugaban Majalisar Dattawan Najeriyar Godswil Akpabio da cin zarafinta ta hanyar nemanta da lalata.Domin jin yadda tsarin na Kiranyen yake...Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Abba Hikima, ƙwararren lauya a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Dr Auwal kan ɗauko hayar sojoji don horas da sojojin Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci
26/03/2025 Duração: 03minGwamnatin Najeriya ta ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga wasu ƙasashen duniya, domin horas da sojojin ƙasar wajen yaƙi da ta’addanci, da kuma yin ƙundunbala wajen ceto mutanen da ‘yan ta’addan ke yin garkuwa da su. Ministan Tsaron Najeriya Badaru Abubakar ne ya sanar da matakin, a lokacin da yake ƙaddamar da aikin fara horas da kashin farko na sojojin Najeriyar a Kaduna. A kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Auwal Aliyu Abdullahi, mai magana da yawun Kwamitin musamman na kula da walwalar tsaffin sojoji a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu.............
-
Barista Al-Zubair kan matakin daina holin waɗanda ake zargi da ƴansanda ke yi
25/03/2025 Duração: 03minSufeta Janar na ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun, ya jaddada umarnin Antoni Janar na ƙasar, kan haramcin holin waɗanda ake zargi da aikata laifuka da jami’an tsaro ke yi ga manema labarai, ba tare da an hukuncin kotu ba. Ya ce a lokuta da dama jam’an tsaro basa iya gabatar da hujjoji kan zarge-zagen a gaban kotu, duk da cewa an nuna wa duniya fuskokinsu, lamarin da ya ce ya sabawa dokokin kare hakkin ɗan adam. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tsakanin Khamis Saleh da Barista Al-Zubair Abubakar........
-
Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya kan cikar ECOWAS shekaru 50
24/03/2025 Duração: 03minYayin da ƙungiyar ECOWAS ke cika shekaru 50 a wannan mako, mun shirya muku rahotanni da hirarraki daban-daban dangane da gudunmawar da ƙungiyar ta bayar a cikin waɗannan shekaru. Daga cikin su akwai rawar da dakarun ECOMOG suka taka wajen magance rikice-rikice da aka samu a ƙasashen Liberia da Saliyo.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya, ɗaya daga cikin sojojin da suka yi aikin samar da zaman lafiyar. ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Dakta Idris Harbau akan dakatar da sayar wa Ɗangote ɗanyen mai
21/03/2025 Duração: 04minA ranar Larabar da ta gabata, matatar mai ta Ɗangote a Najeriya ta sanar da dakatar da sayar da mai da Naira ga 'yan kasuwa.Tuni dai lamarin ya haifar da fargaba a kan yiwuwar fukantar ƙarin farashin litar mai, bayan sauƙin da ‘yan Najeriya suka samu. Sai dai kamfanin ya ce matakin na wucin gadi ne, har sai an samu daidaito tsakaninsa da kamfanin NNPCL a kan adadin ɗanyen man da yake saye daga wurinsa da Naira.Kan wannan batu Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, masanin tattalin arziƙi a Najeriya.Latsa alamar sauti don sauraren hirar:
-
Dalung kan matakin dakatar da gwamnan Rivers da shugaba Tinubu ya ɗauka
20/03/2025 Duração: 03minƘungiyar Lauyoyin Najeriya ta bayyana rashin amincewar ta da matakin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka, na dakatar da gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar, tare da naɗa kantoman soji. Kungiyar tare da jam’iyyun adawa da kuma wasu masu sharhi na cewa matakin ya saba dokar ƙasa. Dangane da wannan matsayi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin shari’a Barr Solomon Dalung. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........
-
Dakta AbdulHakim Funtua kan harin Isra'ila da ya hallaka Falasɗinawa sama 400
19/03/2025 Duração: 03minƘasashe da hukumomi na ci gaba da yin tsokaci daban daban a kan halaka Falasɗinawa sama da 400 da Isra’ila ta yi jiya Talata a Gaza, lamarin da ya rusa yarjejeniyar tsagaita wutar da ta shafe watanni biyu tana aiki a yankin. Wani batu da ya ɗauki hankali bayan harin kuma shi ne, alwashin da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha na amfani da ƙarfi fiye da na baya wajen ƙwato ragowar mutane kusan 60 da ƙungiyar Hamas ke riƙe da su a Zirin na Gaza. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Nura Ado Suleiman da Dakta AbdulHakim Garba Funtua kan wannan lamari......
-
Tattaunawa da Dakta Kurfi kan hada-hadar kuɗaɗen Crypto a Najeriya
18/03/2025 Duração: 03minAlƙaluma na nuni da cewa amfani da kuɗaɗen Crypto na daɗa samun karɓuwa a ƙasashen Yankin Kudu Da Saharar Afrika musamman ma Najeriya, inda a bara wani rahoto ya ce a tsakanin 2023 zuwa 2024, yawan kuɗaɗen Crypton da aka yi hada-hadarsu ya kai na Dalar Amurka biliyan 59. Wannan ya sa wasu ƙwararru bai wa mahukuntan Najeriyar shawarar, kamata yayi su rungumi sauyin domin amfana da shi a maimakon ƙoƙarin daƙile kasuwar Crypton, saboda illolin da suka ce na tattare da ita. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Nura Ado Suleiman da Dakta Ƙasim Garba Kurfi, masanin tattalin arziƙi a Najeriya..............
-
Mahamadou Gamatche kan saukin ƙarancin mai a Jamhuriyar Nijar
17/03/2025 Duração: 03minRahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce an fara samun saukin karancin man fetur da aka fuskanta a kwanakin da suka gabata, abinda ya jefa jama'a da dama cikin halin kunchi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Muhammadu Gamatche, shugaban gamayyar kungiyoyin masu motocin sufuri ta kasa a Nijar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana
-
Malam Sirajo Issa kan rahoton taron ƙasar da aka yi a Nijar
14/03/2025 Duração: 03minKwanai bayan miƙa rahoton taron ƙasar da aka yi a Jamhuriyar Nijar, mutane na ci gaba da gabatar da ra'ayoyin su akai. Malam Sirajo Issa na ƙungiyar Mojen ya ce basa goyon bayan taron.
-
Farfesa Balarabe Sani Garko kan magance matsala mutuwar mata da jarirai
12/03/2025 Duração: 02minGwamnatin Najeriya ta bai wa jihohin kasar Dala biliyan guda domin amfani da shi wajen magance matsalar da ake samu na mutuwar mata da jarirai lokacin haihuwa.Ministan lafiyar kasar Mohammed Pate ya sanar da haka.Domin jin tasirin da zai yi,Bashir Ibrahim Idriss ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Tattaunawa da shugaban Amnesty a Najeriya kan kwato kuɗaɗen da EFCC ta yi
11/03/2025 Duração: 03minHukumar EFCC dake yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sanar da kwato kuɗaɗen da suka kai naira Triliyan guda a shekarar da ta gabata, abinda ke nuna irin nasarar da ta samu, baya ga samun nasara a kotu a shari’o’in da suka kai sama da 4,000.Dangane da wannan nasarar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Isa Sanusi, Daraktan Ƙungiyar Amnesty a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiya hirar...........
-
Dokta Elharun Muhammad kan ƙoƙarin sasanta tsakanin AES da ECOWAS
10/03/2025 Duração: 03minShugaban Ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya ƙaddamar da wani shirin diflomasiya domin shawo kan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, wadanda suka fice daga cikin ƙungiyar ECOWAS.A ƙarshen makon da ya gabata, shugaban ya ziyarci waɗannan ƙasashe guda uku, inda ya gaba da shugabannin su.Dangane da tasirin wannan ziyarar, Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da Dr Elharun Muhammad na Cibiyar kula da manufofin ci gaban ƙasashe dake Kaduna, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Dakta Khadija Abdullahi kan Ranar Mata ta Duniya
07/03/2025 Duração: 03minA Asabar ɗin nan ce ake bikin Ranar Mata ta Duniya, wanda aka fara gudanar da ita fiye da shekaru 100 da suka gabata, domin kare haƙƙoƙin matan da kuma samar da daidaito tsakaninsu da takwarorinsu maza.Taken ranar bana dai shi ne ‘Buƙatar gaggauta cimma muradin haƙƙoƙin na mata'. A kan wannan rana ta musamman da aka ware wa Mata, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Khadija Abdullahi Iya.........
-
Tattaunawa da Khadija Saulawa kan zargin Akpabio da neman lalata da Natasha
06/03/2025 Duração: 02minƘungiyoyin mata daban daban na ci gaba da gudanar da zanga zanga dangane da zargin cin zarafin da Sanata Natasha Uduaghan ke yi kan shugaban Majalisar dattijan ƙasar Godwill Akpabio na neman yin lalata da ita, wanda ya sanya matan miƙa buƙatar murabus ɗinsa, kodayake jami'an tsaro sun yi amfani da hayaƙi mai sanya ƙwalla wajen tarwatsa dandazonsu. Dangane da yadda tarin mata ke fuskantar cin zarafi walau a wuraren ayyuka koma a tsakar gari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Khadija Suleiman Saulawa wata mai rajin kare haƙƙoƙin mata a Najeriya ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Barau Jibril kan tawagar da ECOWAS za ta sake aikewa ƙasashen AES
05/03/2025 Duração: 03minMajalisar dokokin Ƙungiyar ECOWAS ta sake kafa wani sabon kwamiti da zai ziyarci ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, domin tattaunawa da hukumomin sojin dake mulki a ƙasashen 3 waɗanda suka samar da ƙawancen AES. Mataimakin shugaban Majalisar Ɗattawan Najeriya, Sanata Barau Jibril ya bayyana haka bayan wani zaman na musamman da Majalisar ECOWAS ta gudanar a birnin Lagos, dangane da wannan ne kuma suka zanta da Bashir Ibrahim Idris.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Ƙananan hukumomi 25 kacal ne suka miƙa asusun su na banki - Gwamnatin Najeriya
04/03/2025 Duração: 03minGwamnatin Najeriya ta ce shugabannin ƙananan hukumomin ƙasar sama da 700, sun gaza wajen gabatar da asusun ajiyar da za ta rinƙa zuba musu kuɗaɗensu kowane wata. Babbar jami'ar da ke kula da asusun ƙasar Oluwatoyin Sakirat Madein ta ce daga cikin ƙananan hukumomi 774 da ake da su a ƙasar, 25 ne kacal suka gabatar da asusunsu. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tintiɓi Hon Saleh Yahya Taki, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kazaure da ke jihar Jigawa.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..............
-
Dr Bashir Nuhu Mabai kan janyewar Isra'ila a tattaunawarta da Hamas
03/03/2025 Duração: 03minTattaunawa tsakanin wakilan Isra'ila dana Hamas domin amincewa da shiga rukuni na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu ta katse a birnin Alqahira na Masar bayan gaza cimma daidaito. Tuni Isra'ila ta dakatar da shigar da kayakin agaji zuwa yankin Gaza da ƙungiyoyi ke jagorantar kaiwa wanda aka tattara daga ƙasashen Larabawa ga Falasɗinawan yankin da ya yi fama da yaƙin kusan shekaru 2, lamarin da ke da nasaba da yadda Hamas ta ƙi amincewa da ƙara wa'adin rukunin farko na yarjejeniyar a gefe guda Isra'ila ta ƙi amincewa da shiga rukuni na biyu, wanda ya sanya tuni Isra'ilan ta fara dawo da hare-hare zuwa wasu yankuna ciki har da Rafah.Dangane da wannan matsala Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Bashir Nuhu Mabai na jami'ar Dutsinma ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Farfesa Mansur Yelwa kan muhimmancin azumin watan Ramadan ga Musulmai
28/02/2025 Duração: 03minGobe Asabar ke zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1446 dai-dai da 1 ga watan Fabrairun 2025, abinda ke nufin al'ummar musulmi a faɗin duniya za su fara da gudanar da ibadar azumi, wanda ake gudanarwa duk shekara. A lokacin watan Ramadan al'ummar musulmi kan ruɓanya ayyukan ibadar da suke gudanarwa, domin neman dace wa a wurin Allah SWT, tare da samun falala mai tarin yawa.Kan hakan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Mansur Isa Yelwa fitaccen malamin addinin musulinci a Najeriya.Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar...
-
Alhaji Shu'aibu Idris kan rage farashin mai da matatar Dangote ta yi
27/02/2025 Duração: 03minA yayin da ake gab da fara azumin Ramadan, Matatar Mai ta Ɗangote da ke Najeriya ta sanar da rage farashin litar man fetur da take sayar wa ƴan kasuwa daga Naira 890 zuwa Naira 825, rahusar da ta fara aiki daga yau Alhamis, 27 ga watan Fabairu. Kan hakan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Shu'aibu Idris.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar...