Bakonmu A Yau

Tattaunawa da Dakta Kurfi kan hada-hadar kuɗaɗen Crypto a Najeriya

Informações:

Sinopse

Alƙaluma na nuni da cewa amfani da kuɗaɗen Crypto na daɗa samun karɓuwa a ƙasashen Yankin Kudu Da Saharar Afrika musamman ma Najeriya, inda a bara wani rahoto ya ce a tsakanin 2023 zuwa 2024, yawan kuɗaɗen Crypton da aka yi hada-hadarsu ya kai na Dalar Amurka biliyan 59. Wannan ya sa wasu ƙwararru bai wa mahukuntan Najeriyar shawarar, kamata yayi su rungumi sauyin domin amfana da shi a maimakon ƙoƙarin daƙile kasuwar Crypton, saboda illolin da suka ce na tattare da ita. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Nura Ado Suleiman  da Dakta Ƙasim Garba Kurfi, masanin tattalin arziƙi a Najeriya..............