Bakonmu A Yau

Barista Abba Hikima kan tsarin kiranye ga ƴan majalisu a dokokin Najeriya

Informações:

Sinopse

A farkon makon nan, Hukumar Zaɓen Najeriya INEC, ta ce ba a kammala cika ƙa'idojin da kundin tsarin mulki ya gindaya ba, a kan tsarin kiranyen da ake ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattijai. INEC ta bayyana haka ne, bayan da ta fara nazari akan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata na nemn yi wa Sanata Natasha yankan ƙauna, wadda a kwanakin baya ta zargi shugaban Majalisar Dattawan Najeriyar Godswil Akpabio da cin zarafinta ta hanyar nemanta da lalata.Domin jin yadda tsarin na Kiranyen yake...Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Abba Hikima, ƙwararren lauya a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.