Bakonmu A Yau

Dr Auwal kan ɗauko hayar sojoji don horas da sojojin Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci

Informações:

Sinopse

Gwamnatin Najeriya ta ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga wasu ƙasashen duniya, domin horas da sojojin ƙasar wajen yaƙi da ta’addanci, da kuma yin ƙundunbala wajen ceto mutanen da ‘yan ta’addan ke yin garkuwa da su. Ministan Tsaron Najeriya Badaru Abubakar ne ya sanar da matakin, a lokacin da yake ƙaddamar da aikin fara horas da kashin farko na sojojin Najeriyar a Kaduna.  A kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Auwal Aliyu Abdullahi, mai magana da yawun Kwamitin musamman na kula da walwalar tsaffin sojoji a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu.............