Informações:
Sinopse
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episódios
-
Kwamared Nuhu Abayo Toro: Kan matatar mai ta Fatakwal
10/12/2024 Duração: 03minƘungiyar Kwadago ta Najeriya ta ziyarci matatar man fetur ta birnin Fatakwal bayan gwamnatin ƙasar ta ce matatar ta fara aiki gadan-gadan. Domin jin yadda wannan matata ta fara aiki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Kwamare Nuhu Abayo Toro, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar kwadagon da suka ziyarci matatar.Ku lata alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Irbaɗ Ibrahim: Yadda John Mahama ya lashe zaɓen Ghana
09/12/2024 Duração: 03minAn kammala zaɓen shugaban ƙasar Ghana, ba tare da fuskantar wata matsala ba, duk da cewa an yi hasashen za'a iya fuskantar tashin tashina a lokacin zaɓen. Sakamkon zaɓen na ƙarshen mako ya nuna cewa tsohon shugaban kasa John Mahama ne ya lashe saben, kuma tuni ɗan takaran jam’iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia ya taya shi murya, abin da ke nuni da cewa ya amince da shan kaye.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris tare da Alh. Irbaɗ Ibrahim, masanin siyasa a Ghana
-
Ambasada Abubakar Chika kan martanin da ake maidawa na kifar da gwamnatin Assad
09/12/2024 Duração: 03minƘasashen duniya sun fara mayar da martani dangane da nasarar da ƴan tawaye suka samu na karɓe iko da birnin Damascus tare da tserewar shugaba Bashar Al Assad. Yayin da wasu ke murna dangane da kawo ƙarshen Assad a karagar mulki, wasu kuma na bayyana damuwa akan makomar yankin Gabas ta Tsakiya. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Chika. Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Mun biya ƴan bindiga kafin mu yi noma amma sun hana mu girbi - mazauna Zamfara
05/12/2024 Duração: 03minMazauna yankunnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na ci gaba bayyana irin halin kuncin rayuwa da suka samu kansu sakamakon yadda suke biyan ƙudi ga ƴan bindiga kafin su yi noma a daminar da suka gabata, yanzu kuma lokacin girbi ƴan bindigar sun hana su zuwa girbi da kwaso amfanin gonar sai sun biya.Wannan matsala ta yi sanadiyar talauta akasarin mutanen da ke wannan yankin. Dangane da wannan batu ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, kuma ga abinda ya shaida masa.