Informações:
Sinopse
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episódios
-
Tsarin tazarar Iyali ya fara samun karɓuwa a yankunan karkara
06/01/2025 Duração: 09minShirin lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu bisa al’ada kan taɓo batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ko kuma a lokuta da dama ya lalubo ƙalubalen da fannin lafiyar ke fuskanta don ankarar da mahukunta da nufin ɗaukar matakan gyara. A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tazara ko kuma tsarin iyali ko Family Planning wanda ke sahun shawarwarin kiwon lafiya da ke ganin kakkausar suka musamman a arewacin Najeriya wala’alla saboda yadda tsarin ya ci karo da al’adun al’ummomin wannan yanki, sai dai a baya-bayan nan alamu na nuna yadda wannan tsari ke samun karɓuwa gadan-gadan.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
-
Cutar sanƙarau ta fara fantsamuwa a sassan jihar Maradi ta Nijar
30/12/2024 Duração: 09minA wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda aka samu ɓarkewar cutar sankarau a wata Makaranta da ke jihar Maradin Jamhuriyar Nijar, cutar da tuni ta harbi tarin ɗalibai, a wani yanayi da masana ke gargaɗi kan haɗarin da ke tattare da wannan cuta musamman nau’in wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi. Kafin yanzu akan ga ɓullar cutar sanƙarau ne a lokaci na zafi sai dai a shekarun baya-bayan nan ana ganin yadda wannan cuta kan sauya salo tare da ta’azzara a lokacin sanyi wadda masana ke ganin ta na da haɗari matuƙa a wasu lokutan illarta kan zarta wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi, kasancewarta mai saurin kisa matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............
-
Barazanar da hunturu ke yi ga keɓantattu ko kwantattun cutuka
23/12/2024 Duração: 09minShirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda lokacin sanyi ko kuma hunturu kan zo da wasu keɓantattu ko kuma tayar da wasu kwantattun cutuka. Nau’ikan cutukan da suke barazana ko kuma tashi a irin wannan lokaci na hunturu sun ƙunshi mura ko tari, ko ciwon hakori baya ga saɓar fata kana yawan fitsari ko cutuka masu alaƙa da zuciya yayinda cutuka irin sikila ko asma kan tashi duk dai a wannan lokaci. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......
-
Yadda ƙungiyar ALIMA ta Faransa ke taimakawa wajen yaƙi da cutar yunwa a Najeriya
16/12/2024 Duração: 09minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan ta’azzarar cutar Tamowa ko kuma rashin sinadaran abinci mai gina jiki da ke addabar ƙananan yara a Najeriya, a wani yanayi da asusun UNICEF ke cewa duk yaro 1 cikin 3 na fama da matsalar ƙarancin abinci a ƙasar, wanda ke wakiltar kashi 37 cikin 100 na yawan yaran ƙasar ko kuma adadin yara miliyan 6. Duk da cewa tsawon lokaci wannan cuta ta ɗauka ta na addabar yara a Najeriyar, a wannan karon cutar ta tsananta a jihohin arewacin ƙasar wanda masana suka alaƙanta da matsaloli masu alaƙa da rashin tsaron da ya hana jama’a noma da kuma gushewar damunar bana da wuri, lamarin da ya ƙara yawan yaran da ke fama da cutar ta Tamowa ko kuma yunwa, dalilin da ya ja hankali ƙungiyoyin agaji da dama ciki har da ALIMA wato Alliance for International Medical Action ta Faransa wadda ke bayar da agajin lafiya a ƙasashe 13 ciki har da Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
-
Irin kulawar da ya kamata iyaye su bai wa ƴaƴansu a yanayi na hunturu
09/12/2024 Duração: 10minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan cutukan da ke barazana a lokacin sanyi, baya ga shawarwari kan yadda iyaye za su kula da lafiyar yaransu a irin wannan lokaci, musamman ganin cewa yaran ne sanyi ya fi yiwa illa fiye da manya. Dai dai lokacin da iskar hunturu ta fara kaɗawa a sassan jamhuriyar Nijar, jihar Difffa na sahun jihohin da wannan matsala ke tsananta matuka ta yadda a kowacce shekara ake ganin tarin waɗanda sanyi kan yiwa lafiyarsu illa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......
-
Adadin masu kamuwa Cancer zai ninka sau 10 a Najeriya- Masana
02/12/2024 Duração: 10minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda cutar Cancer ko kuma Daji ko Najeriya ke ta'azzara a Najeriya a wani yanayi da ake da ƙarancin wayar da kai kan cutar duk kuwa da illar da ta ke ci gaba da yiwa jama'a. Hankulan masana a ɓangaren kiwon lafiya ya tashi ne matuƙa bayan hasashen da ke nuna yiwuwar alƙaluman masu kamuwa da cutar duk shekara a Najeriyar da yawansu ya kai dubu 70 ya iya ruɓanyawa fiye da ninki 10 nan da shekaru ƙalilan masu zuwa a ƙasar, a wani yanayi da har yanzu jama'a ke jahiltar cutar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Matsalar mace-macen mata masu juna biyu ta sake ta'azzara a Nijar
02/12/2024 Duração: 10minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matsalar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai walau a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki, matsalar da ke tsananin ta'azzara a Jamhuriyyar Nijar bayan da alƙaluma suka nuna yadda matsalar ke kwan-gaba-kwan-baya sakamakon dawowarta a baya-bayan nan bayan daƙileta a shekarun baya. Masana sun alaƙanta matsaloli masu alaƙa da rashin cin abinci mai gina jiki ko kuma rashin kulawar lafiya baya da rashin garkuwa mai ƙwari ga matan a jerin manyan dalilan da kan sabbaba mace-macen matan masu juna.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda ake samun ƙaruwar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a
25/11/2024 Duração: 10minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya nazarci yawaitar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a da ake ganin ta’azzararsu a wannan lokaci musamman a sassan Najeriya a wani yanayi da matsi ko kuma tsadar rayuwa ke ci gaba da galabaitar da jama’a. Dai dai lokacin da masana ke alaƙanta wannan matsala ta mutuwar far ɗaya da wasu kwantattun cutuka da yanayi kan tayar da su a lokaci guda, wani bincike baya-bayan nan ya danganta tsananin damuwa da yawaitar tunane-tunne halin rayuwa a matsayin ummul aba’isin kamuwa da wasu cutuka da ke kisan jama’a. Tuni dai masana a ɓangaren kiwon lafiya suka tsananta kiraye-kirayen ganin jama’a sun mayar da hankalin wajen sanin halin da lafiyarsu ke ciki don kaucewa mutuwar ta kwaf ɗaya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......
-
Lafiya Jari ce: Illar da hayaƙin girki ke yiwa lafiyar idon Mata
11/11/2024 Duração: 10minA wannan makon shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani gargaɗin masana game da illar hayaƙi ga lafiyar jama’a a wani yanayi da masanan ke ganin mazauna garuruwa irin Kano da Sokoto da Kwara baya ga kaso mai yawa na jihohin arewacin Najeriya na cikin haɗarin kamuwa da cutukan masu alaƙa da numfashi sakamakon yadda suka dogara da itace ko kuma gawayi wajen yin girki. A ɓangare guda wasu ƙwararrun na ganin matan da suka shafe lokaci suna girki da itace ka iya fuskantar matsalar ido, tambayar a nan ita ce ko matan na da masaniya kan illar hayakin girki ga lafiyar idonsu? Ku biyo mu a cikin shirin don sauraren mahangar masana da kuma yadda Mata ke kallon illar ta hayaƙin girki ga lafiyarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
-
Yadda cutar kwalara ta addabi wasu jihohin arewacin Najeriya
04/11/2024 Duração: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar Kwalara ko Amai da Gudawa da ta afkawa wasu jihohin Najeriya, inda ta haifar da asarar ɗumbin rayuwa tun bayan ɓullarta a farkon wannan shekara ta 2024
-
Ƙuncin rayuwa na jefa ɗimbin ƴan Najeriya cikin tsananin damuwa - Rahoto
28/10/2024 Duração: 09minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan matsalar damuwa mai dankwafarwa ko tsananin damuwa da ake kira Depression, cutar da ake ganin ta’azzararta a baya-bayan nan tsakanin ƙasashe masu tasowa musamman waɗanda ke fama da matsi ko kuma ƙuncin rayuwa. Wasu bayanan ƙwararru yayin bikin ranar lafiyar ƙwaƙwalwa da ya gudana a farkon watan nan, ya nuna yadda matsi da ƙunchin rayuwa ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya a tsananin damuwar ko kuma damuwa mai dankwafarwa, matsalar da likitoci suka yi gargaɗin cewa ka iya kaiwa ga taɓin ƙwaƙwalwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........
-
Yadda mutane ke kauracewa yin gwaje-gwajen lafiya na wajibi
21/10/2024 Duração: 09minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon yayi duba ne kan ƙalubalen da fannin lafiya ke fuskanta na yadda ake gani a halin yanzu jama’a ke tsoro ko kuma kaucewa gwaje-gwajen lafiya ciki kuwa da har da wajibi da suka ƙunshi hawajini da nau’in jini ko kuma rukuninsa duk kuwa da muhimmancin hakan ga lafiyarsu. A baya-bayan nan bincike ya gano yadda jama’a kan kaucewa yin gwaje-gwaje kama daga na wajibi ko kuma a lokacin kamuwa da cutuka, walau ko saboda tsoron gano wasu nau’in cutuka da ke tare da su ko kuma wani dalili na daban.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......
-
Illar shan magani ba tare da shawarar masana kiwon lafiya ba
14/10/2024 Duração: 09minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar shaye-shayen magunguna ba bisa ka'ida ko kuma shawarwarin masana kiwon kiwon lafiya ba, wadda hakan ke haifar da matsaloli da dama a jikin dan'adam. 14/10/2024
-
Illar da hayaƙin taba sigari ke da shi ga lafiyar al'umma
07/10/2024 Duração: 10minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar zuƙar taba sigari a cikin al'umma saɓanin wasu keɓantattun wurare da doka ta tanada. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a duk shekara sama da mutane miliyan 8 ne ke mutuwa sanadiyar shakar hayakin taba sigari kuma daga cikin wancan adadi, akwai sama da yara dubu 65 waɗanda lamarin ke shafa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
-
Yadda ake samun ƙaruwar masu fama da cutar amasonin jini
30/09/2024 Duração: 09minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda ake ganin ƙaruwar masu fama da cutar amasonin jini, ko Sickler ko kuma Emasi, batun da ke da alaƙa ta kai tsaye da auratayyar da ake yi tsakanin masu nau’ikan jinin da masana ke gargaɗi kan illar da hakan ke da shi ga ƴaƴan da za su haifa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
-
Tsanantar cutar ƙoda da abubuwan da ke haddasa ta a tsakanin al'umma
23/09/2024 Duração: 09minA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan abubuwan da ke haddasa cutar koda, la'akari da yadda cutar ke tsananta a wannan lokaci musamman a kasashe irin Najeriya, sabanin a lokutan baya da ba kasafai ake ganinta ba, baya ga karancin wuraren wankin kodar da ake fama dasu wato dialysis centers a turance. Wani bincike na baya-bayan nan na nuni da cewa cutar koda ita ce ta 10 cikin cututtukan da ke kan gaba wajen haddasa mace-mace a fadin duniya, inda binciken ya nuna cewa kuma tana shafar kusan kashi 10 na al'ummar duniya, wanda a halin yanzu sama da mutane miliyan 850 ke fama da ita.
-
Abubuwan da ke haddasa tsinkewar laka ga ɗan Adam
20/09/2024 Duração: 09minShirin lafiya jarice na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar katsewar laka wacce ke iya afkuwa a sanadiyar hadarin mota ko makamantansu da rikice-rikice ko fadowa daga wurare masu tudu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Yawaitar masu fama da lallurar laka a sassan Najeriya
16/09/2024 Duração: 09minA wannan mako shirin zai mayar da hankali game da cuta ko kuma ‘‘lalurar katsewar Laka’’ wato Spinal cord Injury, lalurar da a baya-bayan nan alƙaluma ke nuna yawaitar masu fama da ita a sassan Najeriya, walau sakamakon haɗarin mota ko rikici dama sauran dalilai. Yayin bikin ranar wayar da kai game da lalurar ta Laka da ke gudana a kowanne wata na Satumba, da a wannan karon aka yiwa take da ‘‘ Kawar da tarzoma a matsayin hanyar kawar da laka’’ masana sun ce baya ga haɗurran mota hanyoyi da dama na haddasa wannan lalura ta laka.
-
Yadda cutar borin gishiri ke addabar mata masu juna biyu a Jamhuriyar Nijar
09/09/2024 Duração: 10minA wannan makon shirin zai mayar da hankali kan cutar borin gishiri ko kuma kumburin da mata ke fama da ita yayin da suke da dauke da juna biyu, wacce kuma a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. Wannan cuta a Jamhuriyar Nijar na daga cikin wacce ke ciwa hukumomi tuwo a kwarya ganin yadda mata sama da dari biyar da 30 cikin kowace mace dubu daya ne kamuwa da wannan cuta, kuma sama da 50 ke rasa ransu a sanadiyarta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
-
Ƙaruwar ƙananan yara da ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki
02/09/2024 Duração: 10minA wannan makon shirin zai mayar da hankali kan ƙaruwar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa ko kuma Tamowa a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci, cikinsu kuwa har da Nijar, ƙasar da alƙaluman 2021 ke cewa akwai ƙananan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 akalla miliyan 1 da dubu 800 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. A baya-bayan nan anga ƙaruwar yaran da ke fama da cutar Tamowa ko da ya ke har yanzu akwai ƙaranci sani game da cutar, kan hakan mu ka fara da tuntuɓar Dr Fayuz Mu’azu likitan mai kula da ƙananan yara masu fama da cutar Tamowa a jihar Diffa, ya kuma yi mana bayani kan cutar da dalilan da ke haddasata.