Informações:
Sinopse
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episódios
-
Hatsarin da ke cikin amfani da maganin ƙwari wajen adana kayan abinci
22/07/2024 Duração: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani da ma sshigowa da shi Najeriya, bayan da ce bincikenta ya tabbatar da cewa maganin yana haddasa cutuka da suka haɗa da cancer.
-
Tasirin sabbin abinci da aka ƙirƙira wato Synthetic Foods ga lafiyar jama'a
15/07/2024 Duração: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan tasarin nau'ukan abinci da akan ƙirkira a ɗakunan bincike wadanda ake kira Synthetic foods a turance, domin nazari kan illolinsu ko kuma akasi ga lafiyar jama'a, duba da yadda nau'ukan abinci da nomansu akayi ba ko kiwo ke samun ƙarbuwa a wasu kasashen duniya.