Tambaya Da Amsa

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 7:12:33
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Episódios

  • Tambaya da amsa

    09/11/2024 Duração: 19min

    A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku takaitaccen tarihi ne akan yankin Bakasi wanda ke kudu maso kudancin Najeriya da kuma tasirin sa wadda yakai ga samun tababa akansa tsakanin Najeriya da Kamaru. Sai a latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin

  • Amsoshin wasu daga cikin tambayoyi masu sauraren Rfi

    26/10/2024 Duração: 20min

    A cikin wannan shirin ,Nasir Sani ya tattaro tambayoyin ku masu sauraren Rfi hausa,wandada a cikin wannan shirin za ku ji amsoshin wasu daga cikin su.Masu saurare sun bukaci samun karin haske dangane da yarjejeniya a bangaren da ya shafi yankinn  Neja Delta da Gwamnatin Najeriya.Shirin Tambaya da amsa na zuwa maku ne a duk karshen mako daga sashen hausa na Rfi.

  • Tambaya da Amsa:-Taƙaitaccen tarihin Ibrahim Ra'isi tsohon shugaban Iran

    12/10/2024 Duração: 20min

    Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani a wannan mako kamar yadda ya saba ya amsa wasu jerin tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki kuwa har da amsar tambaya kan tarihin Marigayi shugaba Ibrahim Ra'isi na Iran da Allah ya yi rasuwa sakamakon haɗarin jirgin sama cikin shekarar nan.

  • Bayani a kan hotunan da ake bugawa a jikin takardun kuɗi

    05/10/2024 Duração: 19min

    A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan tasirin hotunan mutane ko dabbobi ko na tsirrai da akan sanya a jikin takardun kudi da na kwandaloli.

  • Alfanun siyasar Birtaniya ga kasashen Afrika,ko yaya zaben su ke gudana?

    28/09/2024 Duração: 19min

    A cikin shirin tambaya da amsa, a duk karshen mako,Nasiru Sani kan kawo maku wasu daga cikin amshoshin ku masu saurare.A wannan mako za ku ji amsa dangane da siyasar Birtaniya,da wasu daga cikin amsoshin tambayoyin ku masu saurare.

  • Tasirin da tarzoma ke yi ga tattalin arziƙin ƙasa

    14/09/2024 Duração: 17min

    Shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, domin samun fahimta kan batutuwa ko abubuwan da suka shige muku duhu wanda  ke zuwa muku a kowanne mako kuma a daidai wannan lokaci. Kuma a yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan tasirin da tarzoma ke da ita ne akan tattalin arziki.

  • Amsar tambaya kan salon siyasar Birtaniya da banbancinta da na sauran ƙasashe

    17/08/2024 Duração: 19min

    Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani a wannan mako  ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da aka aika mana, Shirin ya amsa tambaya kan yadda neman ƙarin bayani da wani mai sauraro ya yi kan zubu ko kuma yanayin siyasar Birtaniya dama banbancinta da siyasar da ake gani a ƙasashen da ta mulka.Wannan da sauran tambayoyi na tafe a cikin shirin na wannan mako.

  • Shin yaya duniyar aljanu take da kuma yadda ma'askin dare ke gudanar da aikin sa?

    10/08/2024 Duração: 20min

    A cikin shirin Tambaya da amsa na wannan mako zaku ji fashin baki kan Ma'askin dare, da kuma duniyar aljanu Danna Alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani

  • Ƙarin bayani kan yarjejeniyar SAMOA da ta haifar da cece-kuce a Najeriya

    03/08/2024 Duração: 18min

    Shirin 'Tambaya da amsa' na wannan mako kamar kullum ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aika, masaman ƙarin bayani gameda yarjejeniyar SAMOA da ya haifar da cece -kuce tsakanin gwamnatin Najeriya da ƴan ƙasar masannan malaman addini.

  • Banbanci dake tsakanin siyasar Birtaniya da siyasar kasashen Duniya?

    20/07/2024 Duração: 18min

    A cikin shirin Tambaya da amsa daga Sashen hausa na Rfi,masu sauraro kan aiko da tambayoyin su,wandada muke mika su ga masana da suke yi mana fashin baki a kai.A cikin wannan shirin Nasir Sani ya leko wasu daga cikin tambayoyin masu sauraro.

  • A cikin shirin zaku ji amsar tambaya game da sabon irin masara da aka samar

    13/07/2024 Duração: 20min

    Shirin tambaya da amsa na wannan makon ya amsa tambayoyi da dama da masu saurare suka aiko mana su. Danna alamar saurare don jin masoshin tambayoyin ta cikin shirin tare da Nasiru Sani

  • Bayani a kan ayyunkan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO

    15/06/2024 Duração: 19min

    Shirin 'Tambaya Da Amsa' wanda ya ke zuwa duk mako a wannan tasha zai amsa tambayar da ke neman bayanni a kan ayyukan Hukumar Lafiya ta Duniya,,musamma inda take samun kuɗaɗen gudanar da ayyukanta da kuma yadda taa ke ɗaukar ma'ikata.

  • Amsar tambaya game da muhimmancin taken ƙasa wato National Anthem

    08/06/2024 Duração: 18min

    Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru sani kamar kowanne mako ya na gayyato ƙwararru ne don amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana.  A wannan mako, shirin ya amsa tambaya game da tasirin taken ƙasa da ake kira National Anthem a Turance.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..

  • Tarihin tsohon shugaban Iran Ebrahim Raisi da bayani akan ma'askin dare

    01/06/2024 Duração: 20min

    Shirin tamabaya da amsa na wannan mako zai kawo muku tarihin shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar 19 ga watan Mayun shekarar 2024, tare da bayani akan ma'askin dare kamar yadda aka aiko mana da tambayoyi akansu, sai a kasance tare da mu a cikin shirin.

  • Bayani kan kotun ICC da kuma sammacin kamo firaministan Isra'ila da shugabannin Hamas

    25/05/2024 Duração: 20min

    Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a game da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC da batun sammacin  kama firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da wasu shugabannin ƙungiyar Hamas. Ku latsa alamar sautin donjin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.........

  • Bayani a kan kamanceceniyar mulkin gurguzu da kama-karya

    04/05/2024 Duração: 20min

    Shirin, wanda  ke zuwa muku duk mako a lokacin irin wannan, yana kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wasu daga cikin masu bibiyanmu suka aiko mana ne, kuma a yau, za ku ji amsar tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan salon mulkin gurguzu, da kuma ko da gaske yana  da kamanceceniya da mulkin kama-karya kamar yadda masu kushe shi ke fadi. Sai a kasance tare da  mu.

  • Hukumar samar da wutar lantarki ta yi bayani game da kudin wuta da jama'a za su biya a Najeriya

    13/04/2024 Duração: 20min

    ‘Tambaya Da Amsa’ shiri ne da ke kawo amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Bayan janye tallafin lantarki a Najeriya, hukumar samar da wutar ta yi bayani  game da rukunnai dabam dabam na masu amfani da wuta da abin da za su biya a matsayin kudin wuta. A yi mun ƙarin bayani a kan wadannan rukunnai. Menene ya sa dole sai an kasa al’umma zuwa rukuni -rukuni?

  • Ƙarin bayani kan yakin duniya da yadda za'a kauce wa sake barkewarsa

    30/03/2024 Duração: 20min

    Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a kan yakin duniya da yadda za a kauce wa aukuwar wani yakin duniya.

  • Sanadin katsewar kafofin sadarwa na Internet a nahiyar Afirka

    23/03/2024 Duração: 20min

    shirin a wannnan mako zai ba da hankali ne akan abinda ya kai ga katsewar hanyoyin sadarwa na internet a wasu sassa na Nahiyar Afirka.

  • Karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol

    16/03/2024 Duração: 20min

    Shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa mukua wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, za mu ji karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol. Abokinku, Michael Kuduson ne ke muku lale marhabun.

página 1 de 2