Bakonmu A Yau

Dr. Yahuza Getso kan ta'azzarar matsalolin tsaro a ƙasashen Afirka

Informações:

Sinopse

Matsalolin tsaro na kara ta’azzara a ƙasashen Afirka masamman a Sahel da tafkin Chadi, inda aka ga yadda Boko Haram ke zafafa kai hare-hare a sansanoni da cibiyoyin jami’an tsaro a jihar Barno, yayin da mahara masu ikirarin jihadi suka tsanata kai farmaki a ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Fado, ko a ranar Alhamis ƴan ta’adda sun kashe sojojin Benin kusan 30 a wani hari da suka kai arewacin ƙasar, sai kuma wani hari da ƴan bindiga suka kai fadar shugaban ƙasar Chadi da gwamnati ta  daƙile. A tattaunawarsa da Ahmed Abba, Dr. Yahuza Ahmad Getso masanin tsaro a Najeriya, ya ce duk da yadda ƙasashen ke ikirarin yaƙi da matsalolin tsaro, ba su da cikakkun tsare-tsaren da suka dace a bangaren soji da tafiyar da gwamnati, halisama ba da gaske su ke yi ba.