Lafiya Jari Ce

Tsarin tazarar Iyali ya fara samun karɓuwa a yankunan karkara

Informações:

Sinopse

Shirin lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu bisa al’ada kan taɓo batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ko kuma a lokuta da dama ya lalubo ƙalubalen da fannin lafiyar ke fuskanta don ankarar da mahukunta da nufin ɗaukar matakan gyara. A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tazara ko kuma tsarin iyali ko Family Planning wanda ke sahun shawarwarin kiwon lafiya da ke ganin kakkausar suka musamman a arewacin Najeriya wala’alla saboda yadda tsarin ya ci karo da al’adun al’ummomin wannan yanki, sai dai a baya-bayan nan alamu na nuna yadda wannan tsari ke samun karɓuwa gadan-gadan.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....