Lafiya Jari Ce
Cutar sanƙarau ta fara fantsamuwa a sassan jihar Maradi ta Nijar
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editora: Podcast
- Duração: 0:09:49
- Mais informações
Informações:
Sinopse
A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda aka samu ɓarkewar cutar sankarau a wata Makaranta da ke jihar Maradin Jamhuriyar Nijar, cutar da tuni ta harbi tarin ɗalibai, a wani yanayi da masana ke gargaɗi kan haɗarin da ke tattare da wannan cuta musamman nau’in wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi. Kafin yanzu akan ga ɓullar cutar sanƙarau ne a lokaci na zafi sai dai a shekarun baya-bayan nan ana ganin yadda wannan cuta kan sauya salo tare da ta’azzara a lokacin sanyi wadda masana ke ganin ta na da haɗari matuƙa a wasu lokutan illarta kan zarta wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi, kasancewarta mai saurin kisa matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............