Al'adun Gargajiya

Yadda Hausawa ke ƙoƙarin yin watsi da al'adar amfani da kwarya

Informações:

Sinopse

Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al’ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al’ada tana neman gushewa a tsakanin al’ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al’adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana’ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........